Thursday, 6 September 2018

Shugaba Buhari, matarshi, A'isha da matar gwamnan Kebbi, Dr. Zainab a China

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari tare da uwargida, Hajiya A'isha Buhari da matar gwamnan Kebbi, Dr. Zainab Atiku Bagudu kenan a kasar China inda suka je halartar taron hadin kan kasashen Afrika da China.Hajiya A'isha Buhari ta yi ganawa da wakilan China akan kawar da cutar kanjamau da kuma wayarwa da mutane kai akan cutar a nahiyar Afrika.
No comments:

Post a Comment