Sunday, 30 September 2018

Shugaba Buhari ya amince da ajiye aikin ministar mata

Bayan dawowarshi gida, Najeriya daga kasar Amurka inda ya halarci taron majalisar dinkin Duniya, shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya amince da takardar ajiye aiki ta tsohuwar ministar mata, Jummai A'isha Alhassan, wadda aka fi sani da Mama Taraba.


A cikin wata sanarwa ta hannun me magana da yawunshi, Garba Shehu, ya bayyana cewa ya amince da ajiye aikin na ta sannan kuma, a madadin 'yan Najeriya, yana mata godiya bisa aikin da ta yiwa kasa.

Shugaba Buharin ya bukaci karamar ministar masana'antu data rike aikin ma'aikatar bada wani bata lokaci ba.

No comments:

Post a Comment