Tuesday, 11 September 2018

Shugaba Buhari ya amshi fom din takarar da aka saya mishi

A yau, Talatane, shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya amshi fom din sake tsayawa takara da wata kungiya ta sai mishi, shugwabannin kungiyar sun kaimai fom din har gida kuma sun bayyana farin cikinsu da amincewar da yayi suka saya mishi fom din.


Da yake mika masa fom din a fadar shugaban kasa da ke Abuja, shugaban kungiyar Nigeria Ambassadors Consolidation Network Barista Sanusi Musa ya ce sun ji dadi da shugaban ya amince su saya masa fom din.

A cewar sa, sun sayi fom din ne domin sun gamsu da ayyukan da Shugaba Buhari ke yi na ci gaban Najeriya.


No comments:

Post a Comment