Friday, 7 September 2018

Shugaba Buhari ya dawo daga kasar China

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya bayan ziyarar kwanaki 6 da ya kai kasar China inda ya halarci taron hadin kan kasashen Afrka da Chinar da kuma tattaunawa da mahukuntar kasar dan samawa Najeriya abubuwan alfanu.


Daga cikin abubuwan da shugaba Buharin ya samo daga kasar China akwai bashin dala miliyan dari 328 da za'ayi amfani dasu wajan harkar sadarwa da kuma zuba jari na dala dari 200 da wani kamfanin yin kaya zaiyi a jihohin Kano, Katsina,Abia da Legas, sai kuma maganar gina tashar samar da wutar lantarki dake Mambila.

No comments:

Post a Comment