Tuesday, 4 September 2018

Shugaba Buhari ya fi kashi 80 na 'yan Najeriya lafiya>>Chris Ngige

Ministan ayyuka Chris Ngige ya bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari da cewa, yafi kashi tamanin cikin dari na 'yan Najeriya lafiya, ya kuma kara da cewa yawan shekarun shugaban basa hanashi gudanar da ayyukanshi yanda ya kamata.


Jaridar Punch ta ruwaito Ngige lokacin da yake hira da manema labarai a  Anambra ya kara da cewa, idan yawan shekarune  to ku dubi kasar Malaysia da suka zabi shugaba me shekaru 93.

Kuma shugaba Buhari na da cikakkiyar lafiya, Ngige yace, idan suna zaman majlisar koli, shugaba Buhari yakan zauna na tsawon awanni takwas yayin da su kuma sukan fita hutun shan shayi amma shi yana nan zaune sai dai kawai yasha ruwa.

Ngige yayi kira ga 'yan kabilar Igbo da su marawa shugaban baya a zabe me zuwa lura da cewa be mayar da su saniyar ware ba a sha'anin mulkinshi.

No comments:

Post a Comment