Thursday, 13 September 2018

Shugaba Buhari ya nada sabon shugaban hukumar DSS

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sanar da sabon shugaban hukumar 'yansandan farin kaya da zai maye korarren shugaban, Lawal Daura. Wanda shugaba Buharin ya sanar a matsayin sabon shugaban shine Yusuf Magaci Bichi.


Yusuf dai ya fito daga jihar Kano ne kuma ya jima yana aiki da hukumar ta DSS kamar yanda sanarwar da me magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya fitar ta bayyana.

No comments:

Post a Comment