Friday, 28 September 2018

Shugaba Buhari ya taya zababben gwamnan jihar Osun murna

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya taya zababben gwamnan jihar Osun, Adegboyega Isiaka Oyetola murnar nasarar da yayi a zaben da aka kammala a jihar jiya, Alhamis.


A wata sanarwa da me magana da yawun shugaban kasar, Garba Shehu ya fitar ya bayyana cewa shugaba Buharin na taya zababben gwamnan murna sannan kuma ya jinjinawa Gwamna me barin Gado, Ogbeni Rauf Aregbesola kan irin bautawa jiharshi da yayi na tsawon shekaru 8.

Ya kuma bukaci zababben gwamnan da cewa mutane fa suna bukatar a musu aiki yanda ya kamata dan inganta rayuwarsu.

Ya kuma godewa mutanen jihar ta Osun bisa zaben da sukawa Isiaka.

No comments:

Post a Comment