Sunday, 30 September 2018

Shugaban APC yayi subutar bakin cewa sunyi magudi a zaben Osun

Shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole yayi subutar bakin cewa jam'iyyarsu tayi Magudi a zaben gwamnan jihar Osun da ya gabata.


Oshiomhole na ganawane da manema labarai akan yanda aka gudanar da zaben inda aka jishi yana cewa, domin ci gaban dimokradiyya, kamata yayi ace mutanen da zasu iya jure magudi(sai kuma ya gyara kalamanshi yaci gaba da cewa) faduwa zabene ke fitowa takara.

Wannan lamari da ya faru ya dauki hankulan mutane inda akaita sharhi kala-kala akai.

No comments:

Post a Comment