Wednesday, 12 September 2018

Shugaban kasar Laberia ya buga kwallo da Super Eagles

Shugaban kasar Laberia, George Weah ya buga kwallo tare da tawagar 'yan kwallon kasarshi  a karawar da sukayi da Najeriya jiya Talata a Monrovia. An buga wasanne dan yin ritayar jasin da Shugaban kasar ke sawa me lamba 14.


Weah dan shekaru 51 ya buga mintuna 74 na wasan, kuma a duk lokacin da ya taba kwallo 'yan kallo kan kaure da tafi. Weah dai shine dan kwallon Afrika tilo da ya taba cinye kyautar gwarzon dan kwallon Duniya ta Ballon d' Or.

Wasan ya kare Najeriya na cin Laberia 2-1.


No comments:

Post a Comment