Sunday, 30 September 2018

Shugaban sojan sama ya jewa mahaifan sojan daya rasu a hadatin jirgi gaisuwa

Shugaban sojojin sama, Sadiq Baba Abubakar ya kaiwa mahaifan sojan nan, Muhammad Bello Baba Ari da ya rasa rashi a hadarin jirgin da ya faru ranar Juma'ar data gaba a Abuja.Ya bayyanawa mahaifan marigayin cewa dansu jarumine kuma ya kware sosai a ayyukan da yake yi sannan gwarzo ne wanda baza'a manta dashi ba saboda ya rasu wajan bautawa kasarshi, muna fatan Allah ya kai Rahama kabarinshi.

Daga nan shugaban sojin ya kuma kaiwa sauran sojojin dake kwance a asibiti dalilin raunukan da suka samu a hadarin.

No comments:

Post a Comment