Thursday, 13 September 2018

Tamu ta samu: Wata 'yar Arewa ta samu babban mukamin kasa-da-kasa

Wata 'yar Najeriya daga bangaren arewacin kasar mai suna Farfesa Hauwa Ibrahim ta samu babban mukami da wata kungiyar dake ayyukan ta a kasashe da kuma ke zaune a garin birnin Paris dake rajin tabbatar da samun sahihiyar demokradiyya da kuma labarai masu inganci.


Daily Nigerian ta samu cewa ita dai Farfesa Hauwa yar asalin jihar Bauchi ce kuma babbar Lauya ce da ta lashe kyautar hazaka a shekarar 2005 ta sashen Najeriya watau European Parliament’s Sakharov Prize (Nigeria) a turance.

Ita dai Farfesa Hauwa Ibrahim kafin samun mukamin nata, tana koyawa a makarantar gaba da Sakandare ta Saint Louis University School of Law da kuma Stonehill College dukkan su a kasar Amurka.

Haka ma dai Farfesar ta rike mukamai da dama a kasashe da yawa inda ta samu lambobin girma da shaida mai kyau.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment