Tuesday, 11 September 2018

Tsayawa takarar gwamna da kanin A'isha Buhari yayi a jihar Adamawa ya jawo cece-kuce

Tuni dai ‘kanin Aisha Buhari matar shug aban kasa, ya dauki hoto tare da shugaban Muhammadu Buhari, rike da takardar tsayawarsa takara, batun da wasu ke fassarawa da goyon baya daga fadar shugaban kasa.


Wannan fitar guzan da ‘kanin matar shugaban kasar yayi, na neman rabuwa shugabanin jam’iyar APCn a jihar, da har wasu magoya bayan gwamnan jihar ke cewa ba zata sabu ba, wai bindiga a ruwa.

Hon. Hussaini Gambo Bello, na cikin hadiman gwamnan jihar Adamawan, wanda kuma ya bayyana irin damarar da suka yi don fuskantar wadanda ke neman kayarda gwamnan jihar Adamawa, Sanata Muhammadu Bindow Umar Jibrilla a cikin jam’iyar ta APC.

Tun farko da yake bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar gwamnan Adamawan ga shugabanin jam’iyar APC a jihar, Dakta Mahmood Halilu Ahmad, ya yi gugar zana ne da cewa sun shigo da kafar dama, domin kawo sauyi a jihar.

To sai dai kuma, yayin da ake wannan cece-kucen, shugabanin jam’iyar a jihar dake tare da bangaren gwamnan jihar sun musanta zargin cewa suna tare da wani bangare a wannan dambarwa. Ahmad Lawal shine sakataren tsare-tsare na jam’iyar APC a Adamawa. Ya ce duk wani zabe da za a gudanar a jihar Adamawa zasu tabbatar da cewa anyiwa kowa adalci.

Ya zuwa yanzu dai akwai kusan mutum hudu dake neman fafatawa da gwamnan jihar Adamawan Sanata Bindow Jibrilla, a inuwar jam’iyar APC, wadanda suka hada da tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC, wato Mallam Nuhu Ribadu, wanda kuma lokaci ne ke tabbatar da yadda zata kaya.
VOAhausa.

No comments:

Post a Comment