Wednesday, 26 September 2018

Tsohon mataimakin Gwamnan Kano, Farfesa Hafiz ya sayi fom din takarar Gwamna a PDP

A yayin da tsohon gwamnan jihar Kano, kuma dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya tsayar da sirikinshi, Kabir Tusuf a matsayin dan takarar gwamnan jihar a karkashin jam'iyyar PDP, Kwankwason ya bukaci tsohon mataimakin gwamnan Kano da ya ajiye aikinshi dalilin sabanin da ya samu da Gwamna Ganduje, Farfesa Hafiz Abubakar ya tsaya takarar Sanatan Kano ta tsakiya.


Saidai Rahotanni sun bayyana cewa, Farfesa Hafiz din bai amince da wannan mataki na Kwankwason ba, hakan ya kara fitowa fili yayin da Rariya ta ruwaito cewa, Hafiz din shima ya sayi fom din takarar gwamnan Kano a PDP.

Hakan dai na nufin akwai matsala da ka iya kawo rarrabuwar kawuna a jam'iyyar ta PDP a Kano.

No comments:

Post a Comment