Wednesday, 5 September 2018

Tsohon shugaban 'yansanda Sulaiman Abba ya fito takarar Sanata

Tsohon shugaban 'yansandan Najeriya, Sulaiman Abba ya fito takarar neman kujerar Sanata a karkashin jam'iyya me mulki ta APC.


Abba na neman wakiltar yankin Jigawa ta kudu maso yamma ne a Majalisar dattijai, kujerar da yanzu haka tsohon ma'aikacin hukumar hana fasa kwauri, Sabo na Kudu ke rike da ita, kamar yanda Daily Nigerian ta ruwaito.

A wata hira da yayi da manema labarai, Abba ya bayyana cewa, hukumar 'yan sanda a lokacin mulkinshine ta tilastawa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan amincewa da sakamakon zaben shekarar 2019.

Abba yace musabbabin cireshi daga mukaminshi a wancan lokaci dan yaki bayar da hadin kai wajan canja zaben ne.

No comments:

Post a Comment