Wednesday, 26 September 2018

UEFA ta sake kaddamar da bincike kan PSG

Hukumar Kwallon Kafa ta nahiyar Turai, UEFA ta sake bude bincike kan yadda PSG ta Faransa ke kashe maukdaden kudade.


Wannan na zuwa ne bayan a cikin watan Juni an wanke PSG game da zargin ta da karya dokokin kashe kudade, amma UEFA ta ce, akwai bukatar sake duba lamarin.

PSG dai ta lale kimanin Euro miliyan 222 don kulla kwantirag da dan wasan Brazil Neymar daga Barcelona a cikin watan Agustan 2017.

Sannan ta sake sayen Kylian Mbappe akan Euro miliyan 180 a cikin wannan kakar bayan ya shafe dogon lokaci a kan aro daga Monaco.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment