Thursday, 27 September 2018

UEFA ta wallafa tarihin da wasu 'yan kwallo suka kafa wanda har yanzu Ronaldo da Messi ba su kafa irinshi ba

Taurarin kwallon kafa Cristiano Ronaldo da Lionel Messi sun kasance gwanaye da ke ta kafa tarihi kala-kala suna zarce tarihin da wasu taurarin kwallo na da dana yanzu ke kafawa to saidai duk da wannan kokari nasu hukumar kwallon kafa ta turai UEFA ta fitar da bajintar da wasu taurarin kwallo suka kafa wanda har yanzu Ronaldon da Messi basu kafa irin ta ba.


UEFA ta wallafa bajintar da taurarin kwallo suka kafa wadda Messi da Robaldo basu kafa irin ta ba kamar haka:

Yawan buga kwallo: Messi ya buga gasar cin kofin turai sau 126 shi kuma Ronaldo ya buga sau 158 amma wanda ya kafa bajintar yawan buga wannan wasa shine golan Porto Iker Casillas wanda ya buga wasan sau 179.

Yawan cin kwallaye a wasan karshe: Messi yaci kwallaye biyu ne kawai a wasannin karshe na gasar cin kofin turai da ya taba bugawa a shekarun 2009 da 2011 yayinda shi kuma Ronaldo ya ci kwallaye 4 a wasannin karshe na gasar da ya buga a shekarun 2008 da 2014 yaci kwallaye daya-daya sai kuma a shekarar 2017 yaci kwallaye biyu. Amma wadanda suka kafa tarihin cin kwallaye mafi yawa a gasar sune tsaffin 'yan kwallon Madrid, Alfredo Di Stéfano, Ferenc Puskás, wanda ko wannen su yaci kwallaye 7 a wasannin karshe.

Dan kwallo mafi yawan shekaru da yaci kwallo: Dan wasan AC Milan, Paolo Maldini ya ci wa kungiyarshi kwallo yana da shekaru 36 a wasan karshe da suka buga da Liverpool a shekarar 2005. Sai kuma Francesco Totti da yaci CSKA Moscow a shekarar 2014 yana da shekaru 38.

Dan wasan da ya samu nasara da kungiyoyi daban-daban: Clarence Seedorf ya samu nasara da kungiyoyi irinsu (Ajax 1995, Real Madrid 1998, Milan 2003, 2007) sannan kuma Zlatan Ibrahimovic wanda shima ya samu nasara da kungiyoyi irinsu (Ajax, Juventus, Internazionale, Barcelona, Milan, Paris Saint-Germain) wadannan 'yan wasa biyu duk sun fi Ronaldo da Messi.

Dan kwallon da yaci kwallo cikin kankanin lokaci: Dan wasan Bayern Munich, Roy Makaay ya ciwa kungiyar tashi kwallo cikin sakwanni 10.12 a wasan da suka buga da Real Madrid a shekarar 2007.  Ronaldo ya taba ciwa Real Madrid Kwallo a cikin mintuna 4 a wasan da suka buga da kungiyarshi ta yanzu, Juventus a shekarar 2013, yayin da shi kuwa Messi ya ciwa Barcelona kwallo cikin mintuna uku a wasan da suka buga da Celtic a shekarar 2016 wanda ya kare da sakamakon 7-0.

Dan wasan da yaci kwallo daga guri mafi nisa: Tauraron dan kwallon Manchester United, Ryan Giggs ya ci kwallaye 16 daga guri mafi nisa yayin da Ronaldo kuma yaci guda 13, Messi na da guda 14.

Dan kwallon da yafi cin kwallaye akai-akai: Tauraron dan kwallon kungiyar Bayern Munich, Gerd Müller yafi Ronaldo da Messi yawan cin kwallaye akai-akai a tarihi.

Dan wasan da ya ci kwallaye uku a wasa daya cikin lokaci mafi kankanta: Tauraron dan kwallon kafa na kungiyar Olympique Lyonnais, Bafétimbi Gomis ne yaci kwallaye uku a wasa daya cikin lokaci mafi kankanta a tarihi inda ya ci kungiyar Dinamo Zagreb a shekarar 2011. Ronaldo kuwa yaci kwallaye uku a wasa daya cikin mafi kankanin lokaci na mintuna 12 lokacin yana Real Madrid inda yaci kungiyar Malmao a shekarar 2012, yayin da shi kuwa Messi ya ci kwallayenshi uku a wasa daya cikin mafi kankanin lokaci na mintuna 22, Arsenal ce yaci wadannan kwallaye a shekarar 2010.

Dan wasan da yafi yawan kwallaye a kakar wasa ta gasar ta cin kofin zakarun turai: Dan wasan kungiyar Porto, Radamel Falcao ya ci mata kwallaye 18 a kakar wasan cin kofin zakarun turai ta 2010/11. Messi kuwa a kakar wasan 2011/12 ce yqci kwallaye mafi yawa, 14. Shi kuwa Ronaldo yaci kwallayenshi mafi yawane a kakar wasan 2013/14 inda yaci kwallaye 17.

No comments:

Post a Comment