Wednesday, 12 September 2018

Wani Dalibi Ya Yi Wa Kwankwaso Wakar Turanci, Yace babban burinshi yaga Kwankwason ko sau daya ne

Wani dalibi mai suna Mustapha Abdullahi Inuwa Jauben Gadanya ya yi wa Sanatan kano ta tsakiya Dr Rabiu Musa Kwankwaso waka da harshen Turanci.


Dalibin ya ce bai taba yin waka ba, amma soyayya da kauna da yake ma Rabiu Musa Kwankwaso ta tsakani da Allah suka sa ya tattaro ayyukan Kwankwaso na alkairi da ya yi a Kano da ma kasa baki daya ya dunkule su a waje daya ya saka su acikin wakar sa ta Turanci.

Haka kuma a cikin wakar da ya yi ya farfadi matsaloli da suke samun kasar nan wanda har yanzu shugabanni sun kasa shawo kan matsalar. Amma yana ganin idan aka bawa Kwankwaso dama ya samu mulkin kasar nan to Insha Allah zai kawo karshen dukkanin matsololin da suka damu Nijeriya. 

A cewarsa Kwankwaso mutum ne mai aiki tukuru, mai bibiyar komai da komai, kuma dan ganin kwakwaf.

Dalibin ya kara da cewa duk da dai akwai hamayya ta siyasa, amma duk a haka kowa yasan Dr Rabiu Musa Kwankwaso mutum ne jarumi kuma mai jajircewa wajen aiki da kuma kaunar talakawansa. 

A karshe Dalibin yana rokon duk wani wanda yake da damar yi masa hanyar zuwa ya je ya gaishe da masoyinsa Dr Rabiu Musa Kwankwaso kuma ya ba shi faifan sidin wakar da ya yi masa ta turanci, to don Allah ya taimaka mishi ya kai shi wajen Sanatan domin ya ga Sanatan koda sau daya ne a rayuwarsa. 

Haka kuma Dalibin yace yana fatan wannan wakar da ya yi ta Turanci za ta yi wa Sanatan amfani wajen halin neman zabensa musamman ma a yankin kudancin Nijeriya da ba sa jin yaren Hausa sosai.

Ga lambar wayar Dalibin nan ga duk wanda zai masa hanyar ganawa da Sanata Kwankwason. 08133398649.
Rariya.

No comments:

Post a Comment