Tuesday, 4 September 2018

Wani gwamna a Najeriya ya roki Buhari ya yafewa barayin Najeriya

Gwamnan jihar Ebonyi da ke a kudu maso gabashin Najeriya mai suna David Umahi yayi kira ga gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari da su duba yiwuwar yafewa dukkan 'yan siyasar da ake zargi da laifin wawure dukiyar al'umma.


Mista David Umahi yayi wannan kiran ne a garin Abakalki, babban birnin jihar lokacin da yake jawabi a wurin bude wani taro game da cin hanci da kuma gyaran tarbiyya da da'ar mutanen jihar.

Haka zalika gwamnan ya koka ne game da irin tarin shari'oin da suka shafi cin hanci da rashawa dake a gaban alkalai a kotunan Najeriya inda ya zargi gwamnatin tarayyar da dauko dala ba gammo.

Daga nan ne sai ya shawarci gamnatin da ta yafewa kowa sai ta sake daga farko ta bude sabon shafi.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment