Sunday, 9 September 2018

Wani Hafsan Sojan Nijeriya Ya Bata


Sanarwa daga Dr. Idris Ahmed yace kungiyarsu ta 'Citizens United For Peace and Stability' (CUPS) ta samu sako na bacewar wani babban hafshin sojin Nijeriya Manjo Janar Idris Alkali 


Shi dai Manjor Janar Idris Alkali ya bace ne tun bayan awanni 74 da suka gabata, wayoyinshi gaba daya ba sa tafiya har zuwa yanzu, ya bace ne akan hanyar sa ta zuwa Bauchi daga Abuja.

Ana rokon a isar da wannan sanarwan har zuwa masallatai don a saka wannan babban hafshin soji cikin addu'a akan Allah Ya bayyana shi.

Kamar yadda 'yan uwan shi wannan sojan suka bayar da bayani, sun ce Manjo Janar Idris Alkali yana kan hanyar sa ta zuwa Bauchi ne daga Abuja a cikin motarsa, to tunda ya iso kudancin Jos sai ya bace sakamakon bin diddigi (tracking) na lambar wayoyin sa da jami'an SSS suka yi bayan an kai musu rahoto.

Shi dai Manjo Janar Idris Alkali asalinsa mutumin jihar Yobe ne, kuma an taba hasashen zai zama shugaban sojojin Nijeriya.

Yaa Allah Ka kubutar da wannan bawa naka lafiya a duk halinda ya shiga, Allah Ka tona asirin duk wanda yake da hannu a bacewarsa

Dr. Idris Ahmed.
CUPS.
08/09/2018.

No comments:

Post a Comment