Friday, 7 September 2018

Wani Matashi Da Iyalansa Ya Yi Wa El-Rufa'i Alkawarin Milyan Daya Na Siyan Fom

Wani matashi mai suna Abdullahi Dayyabu da ke zaune a Sabon Gari Zariya ya yi wa Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i alkawarin Naira milyan daya daga cikin kudin siyan fom na tsayawa takarar gwamnan jihar Kaduna a zaben 2019.


Matashin ya bayyanawa RARIYA cewa, ya yi wannan alkawari ne bisa la'akari da irin manufa da kudurin gwamnan jihar Kaduna ga cigaban matasan jihar.

Ya kuma kara da cewa ya dade yana tunanin wacce hanya ce zai ga yana taimakon matasa 'yan uwansa wajen samar masu da hanyoyin dogaro da kai, kwatsam sai Allah ya kawo Malam Nasiru El-Rufa'i, a don haka ya zama wajibi a gare shi da sauran al'ummar jihar Kaduna wajen ganin sun taimaki El-Rufa'i na ganin ya samu nasara don aiwatar da manufofinsa na alheri.
Rariya.

No comments:

Post a Comment