Friday, 7 September 2018

Wani Matashi A Jihar Jigawa Zai Siyar Da Rabin Amfanin Gonarsa Domin Baiwa Buhari Gudunmawa


Alhaji Auwal Usman Wura-wura Mallammadori, Tsohon Shugaban Jam'iyyar Mega Party Na Jihar Jigawa, Kuma Daya Daga Cikin Mabiya Jam'iyyar APC, Ya yi Alkawarin Sadaukar Da Rabin Amfanin Gonarsa Domin Baiwa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Gudummawa.Auwal Usman Ya ce Tunda Yake Bai Taba Yin Noma ba, Sai A Wannan Lokacin Sakamkon Tallafin Da ya Samu Daga Gwamnati Da Kuma  Yawan Kiranye-Kiranyen Da Gwamnatin Shugaba Buhari Take yi Kan Al'umma Su Koma Gona.

Auwal Usman Ya Bayyana Hakan Ne Yayin Da Yake hira Da Wakilin Jaridar RARIYA Na Jihar Jigawa, Inda Ya ce Amfanin Gonan Ya yi Kyau Kuma Zai Ci gaba Da Yin Sana'ar Noma Har Karshen Rayuwasa.
Rariya.

No comments:

Post a Comment