Thursday, 13 September 2018

Wani mutum ya hau kololuwar tangaraho yace bazai sauko ba sai Buhari ya sauka daga mulki

Rahotanni daga shafukan sada zumunta na yanar gizo sun bayyana cewa wani mutum me suna Nurudeen Iliyasu a babban birnin tarayya, Abuja ya dare saman tangaraho inda yace sam ba zai sauko sai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki.


Cikakken rahoton da kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN ya wallafa akan wannan lamari ya bayyana cewa mutumin ya samu me gadin wannan tangaraho yace mai yana so ya hau amma sai me gadin yace mishi a'a kada ya hau.

Bayan da me gadin ya bar gurin sai Iliyasu ya shammaceshi ya dare sama, me gadin yace be ankara ba sai hango Iliyasu yayi ya kai can kololuwar tangarahon, nan da nan kuwa ya garzaya ya gayawa manyanshi abinda ya faru.

NAN ta ruwaito cewa, Iliyasu dan shekara 28 yace yayi hakanne saboda irin halin da kasarnan take ciki, babu aikin yi mutane na kwana da yunwa ga kashe-kashe da ke faruwa.

Yace zai zauna a saman tangarahon dan nuna damuwarshi akan irin wannan abu dake faruwa kuma be damu idan ya mutu saboda yunwa ba, yace yaji likitoci sunce mutum zai iya rayuwa da shan ruwa ba tare da cin abinci ba to abinda zai yi kenan.

No comments:

Post a Comment