Sunday, 16 September 2018

Wannan baiwar Allahn ta musulunta sanadiyyar fim din Hausa

A lokuta da dama, wasu jaruman fina-finan Hausa sukan yi ikirarin cewa fadakarwa suke yi a cikin fina-finan da suke fitowa, saidai wasu 'yan kallo na da ja akan waccan magana inda suke sukar 'yan fin din da gurbata tarbiyya.


Wannan hoton wata baiwar Allahce da ta musulunta sanadiyyar fim din hausa, ta kuma zabi sunan Khadija a matsayin sabon sunanta.

Me shirya fina-finai kuma dan jarida, Nasir S. Gwangwazone ya bayyaba wannan labari inda yayi rubutu kamar haka:

"Alhamdulillah, ta karbi Musulunci a dalilin 'yan fim na Kannywood. Yanzu sunanta Nana Khadijatul Kubhra. Allah Ya amshi wannan aikin alkhairi. Amin."

Muna fatan Allah ya kara fahimtar da ita addini ya kuma karo mana irinta.

No comments:

Post a Comment