Thursday, 27 September 2018

Wasa daya ne kawai Ronaldo bazai buga ba: Zai buga wasan Juventus da Man U

Tauraron dan kwallon kafar Juventus, Cristiano Ronaldo ya tsallake rijiya da baya dalilin jan katin da ya samu a wasan gasar cin kofin zakarun turai da suka buga da Valencia da ya kare Juven na nasara da ci 2-0, hukuncin da UEFA ta fitar akan shi na cewa wasa daya kawai ne bazai buga ba.


Hakan na nufin bazai buga wasan da Juve zata buga da Young Boys ba amma zai buga wasansu da zasu buga da tsohuwar kungiyarshi ta Manchester United a ranar 23 ga watan Octoba.

Ronaldo dai ya samu jan kati wanda dalilin hakan yasa shi zubar da hawaye a fili.

Ba kamar a gasar Frimiya ta kasar Ingila ba da idan aka baiwa dan wasa jan kati take nufinshi kenan ba zai buga wasanni uku na gaba ba, a gasar UEFA wasa da ya ne kawai dan wasa ba zai buga ba har sai masu ruwa da tsaki sun zauna sun auna girman laifin dan wasan suga idan ya kamata a tsawaitamai hukunci ko kuwa a'a, kamar yanda BBCsports suka ruwaito.

No comments:

Post a Comment