Saturday, 29 September 2018

Wata mata tace Ronaldo ya mata fyade

Wata mata 'yar kasar Amurka me suna, Kathryn Mayorga ta bayyana cewa tauraron dan kwallon kafar Juventus, Cristiano Ronaldo ya taba yi mata fyade a shekarar 2009.


Matar ta bayyana hakane a wata jaridar kasar Jamus kamar yanda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

Kathryn Mayorga tace Ronaldo ya gayyaceta wani shagali inda mutane suka halarta, sun nufi wajan wanka, sai Ronaldo ya bata kayan ninkaya ta saka, sai ya bita a baya zuwa dakin da zata canja kayan, ananne abinda ya faru ya faru kamar yanda ta bayyana.

Ta yi ikirarin cewa Ronaldon ya bayyana mata cewa, shi mutumin kirkine amma be san yanda akayi ya aikatamata hakan ba, sannan ya bata makudan kudi dan kada ta kwarmata wannan labari.

Tace amma yanzu, shekaru 9 bayan farwar lamarin tana ta ci gaba da tunawa da kuma samun fargaba akan abinda ya mata shi yasa ta kasa jurewa ta fito ta bayyana wannan labari, ta kara da cewa ta yi dana sanin yadda da wancan alkawari da suka yi na cewa kada ta fadi wannan labari.

Saidai Reuters tace bata iya tantance sahihancin wannan labari ba saboda ta kira wayar matar amma bata amsa ba sannan kuma ta aika da sako shima ba'a dawo mata da amsa ba.

Reuters tace lauyan Ronaldo yace zai yi karan jaridar data wallafa wannan labari saboda ta shiga zarafin sirri na dan wasan.

A shekarun baya, lokacin yana dan shekaru 20 a shekarar 2005 an taba kama Ronaldo a birnin Landan akan zargin yiwa wata mata fyade amma daga baya an sakeshi saboda rashin isassun shaida.

No comments:

Post a Comment