Wednesday, 12 September 2018

Wata sanarwa da Trump ya yi niyyar fitarwa ta kusa janyo yakin duniya na 3

An gano cewar Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya goge wani rubutu da ya yi a shafin Twitter kafin yada shi wanda zai iya janyo yaki da Koriya ta Arewa.


Dan jarida mai bincike da ya kwakwalo abun kunyar Watergate da ya janyo murabus din Shugaban Kasar Amurka Richard Nixon, Bob Woodwar ya fitar da wasu bayanai masu jan hankali.

A littafi na karshe da ya rubuta Woodwar ya tattauna da tashar CBS inda ya bayyana abubuwan da suka faru a Fadar White House.

Woodwar ya ce, Shugaban Amurka Trump ya taba rubutun zai janye iyalan sojojin Amurka da ke aiki a Koriya ta Kudu.

Amma wasu hanyoyi na bayan fage sun mayar da martani irin wanda ba a zata ba.

An bayyana cewar, da zarar Trump ya dauki wannan mataki Koriya ta Arewa za ta ga kamar an shirya yakar ta ne.

Akwai iyalan sojoji dubu 28,000 na Amurka da ke aiki a tsibirin Koriya.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment