Wednesday, 5 September 2018

WHO: Ciwon zuciya na saurin kama masu kiba

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi gargadin cewa kusan kwatar al'umar duniya ne ke cikin hadarin kamuwa da manyan cututtuka, saboda rashin motsa jiki.


An dai wallafa rahoton da WHO ta fitar a mujallar kiwon lafiya Lancet global Health bayan tattaunawa da kusan mutane miliyan 2.

An gano kalilan daga cikin matasa ne ke da karsashi a lokcin da aka yi binciken tsakanin shekarun 2001 da 2016.

Haka kuma WHO ta ce mutanen da ba sa motsa jiki kwata-kwata na cikin hadarin kamuwa da ciwon zuciya, da Ciwon siga ko Diabetes a turance nau'i na 2 da cutar Kansa.

Wani abin tashin hankali game da binciken da aka gudanar, an gano cewa sama da matasa biliyan daya su n cikin hadarin kamuw da cutattuka masu alaka da toshewar magudanar jini da ke karasawa cikin zuciya da farat daya zuciyar ka iya bugawa saboda rashin motsa jiki.
Sama da kashi 40 cikin 100 na Amirkawa ragwaye ne, ya yin da lamarin ya kazanta a wasu kasashe ciki har da gabas ta tsakiya, ya yin da kasashen Iraqi da Saudiyya suka zama ja gaba a yankin.

Binciken ya ce mace daya cikin uku da kuma namiji daya cikin hudu ba su motsa jikinsu yadda ya kamata na akalla minti 150 a mako.

Sannan rabin mutanen da suka kai shekarun girma ba sa tabuka abin azo a gani kamar yadda ya kamata dan kare lafiyarsu ciki har da rashin motsa jiki.

Rahoton ya yi kira ga kasashe su karfafawa mutane gwiwar motsa jiki ta hanyar samar da abubuwan da za su sa mutane yin tafiya da kuma wuraren wasanni na.

Likitoci sun bada shawarar ya kmt a kowacce rana 'yan Adam su dinga matsakaicin motsa jiki, misali tafiyar kasa ko sassarfa da sauransu.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment