Friday, 28 September 2018

'Yan Arewa sunfi 'yan kudu wayewa'

Wani me sharhi akan al'amuran yau da kullun a jaridar Punch yayi magana akan yanda yace mutanen Arewacin kasarnan sunfi na kudu wayau idan aka lura da yanda suke gudanar da al'amuransu na siyasa.

Mutumin me suna Tunji Ajibade yace, yaji hirar da akayi dawasu masu sharhi akan al'amuran siyasar kasarnanne a gidan talabijin na TVC inda suka tattauna akan sanarwar da hukumar zabe ta kasa INEC ta fitar akan rashin karbar katin zabe da mutane basu yi ba inda kididdiga ta nuna cewa a hakan, 'yan Arewa sun tserewa 'yan kudu, nesa ba kusa ba wajan karbar katin zaben.

Yace a Arewa anfi karfafawa mutane gwiwar zuwa karbar katin zaben.

Kuma ya bayar da misali da zabukan jihohin Ekiti da Osun da aka gudanar inda yace kiri-kiri wai sai an ba mutum kudi yake zuwa ya jefa kuri'a a kudancin kasar inda ake ganin sune suka fi ilimin zamani da wayewa amma abin ba haka yake ba a Arewa inda zakaga idan ana zabe mutane na fitowa dan kashin kansu su kada kuri'a.

Yace inda 'yan kudu suka fi auki shine shiga kafafen sadarwa na zamani da gidajen watsa labarai suna babatu amma 'yan Arewa duk da basu cika yin sururai ba da yawa sunfi su yin katabus a siyasance.

A cewarshi wannan yasa yake ganin 'yan Arewa sun fi 'yan kudun wayewa.

No comments:

Post a Comment