Sunday, 2 September 2018

Kukan Karya: 'Yan Najeriya na kwaikwayar kukan Atiku

A makon da ya gabatane labarin kukan da tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar yayi ya karade ko ina a kasarnan, Atikun yayi wannan kukane a lokacin da yaje amsar Fom din tsayawa takarar shugaban kasa na PDP.


Saidai 'yan Najeriya da dama sun dauki kukan na Atiku a matsin wani wasan yara ko kuma shiririta, domin kuwa da dama suna ganin cewa kukan bana gaskiya bane.

Wannan daliline yasa mutane da dama suka rika kwaikwayar kukan na Atiku kamar yanda za'a iya gani a wadannan hotuna.

No comments:

Post a Comment