Saturday, 15 September 2018

'Yan Tawayen Biafara Sun Kona Manyan Motocin 'Yan Arewa A Garin Fatakwat

Wani ganau ba jiyau ba, mai suna Muhammad Bashiru wanda aka fi sani da Dogo, dan asalin jihar Kano amma yana daga cikin masu baiwa motocin kaya suna dauka a garin na Fatakwat, ya tabbatarwa da RARIYA cewa "'yan tawayen sun kawo farmakin ne da misalin 3: 00 zuwa 4: 00 na daren Alhamis, inda suka tasarwa motocinmu na arewa suka kone har 13 a daidai titin Aba.

Muhammad ya kuma yi kira ga gwamnati da sauran kungiyoyi dake yankin Arewa da su sa baki don ganin an yi wa tufkar hanci kasancewar hakan barazana ce ga rayuwarsu a matsayin su na masu harkoki a yankunan kudancin kasar nan.

No comments:

Post a Comment