Manchester United ta sha kashi a hanun kungiyar West Ham United a wasan gasar Frimiya da suka buga yau da ci 3-1, wannan yasa aka fara sukar Mourinho da cewa matsalarshi dai ba akan fadanshi da Pogba ba kadai ta tsaya ba.
Mourinho dai ya jima yana sabani da Pogba wanda yanzu masu sharhi ke ganin ba da Pogban bane kadai me horas da wasan ke da matsala ba watakila ma akwai sauran wasu 'yan wasan.
Kuma da irin wannan sakamakon wasa da ake samu, nana gaba kadan Mourinhon zai tattara komatsanshi ya kara gaba
No comments:
Post a Comment