Monday, 17 September 2018

Yanda mutanen wani kauye a Zanfara suka yi batakashi da 'yan bindigar da suka sace musu 'ya'ya

A farkon makon daya gabata ne wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba da wasu ‘yan mata bakwai, daga garin Girnashe na karmar hukumar Isa a jihar Sokoto.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun gudu da ‘yan matan zuwa dajin Isa mai makwabtaka da Shinkafi ta jihar Zamfara. Inda suka nemi kudin fansa domin sako yaran, a daidai lokacin da jami’an tsaro ke cewa suna shirin ganin sun ceto ‘yan matan.

Da alama dai jama’ar garin basu yarda da maganar jami’an tsaron ba, domin sunyi gayya suka bi sawun ‘yan matan da dukkanninsu ‘yan ‘kasa da shekaru 15 ne da zummar kwato su.

Hakan ya haifar da bata kashi tsakaninsu da ‘yan bindigar da suka yi musu kwantan bauna, lamarin da yayi sanadiyar salwantar rayuka.

Alhaji Bello Aliyu, shine sarkin Rafin Dantasauko babbar gundumar Girnashe. Ya bayyana cewa an sace ‘yan matan guda takwas, an kuma kashe wani direban mota. Hakan yasa wasu ‘yan banga suka bi sawun barayin, inda aka yi bata kashi, an kuma kashe biyar daga cikin ‘yan bangar.

Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da afkuwar lamarin, duk da yake ta ce bada yawunta jama’ar suka tunkari ‘yan bindigar ba.
VOAhausa.

No comments:

Post a Comment