Tuesday, 4 September 2018

Yanda Saraki da mukarrabnshi suka rika addu'ar Allah yasa Buhari ya mutu

Sanata Omo Agege ya fawa kwai akan yanda kakakin majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki da wasu mukarrabanshi su kayi ta addu'ar Allah ya sa shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya mutu.


Agege yayi wannan maganane a mazabarshi dake Sapele a jihar Delta lokacin da yake ganawa da jama'ar shi a kokarin jawo hankalinsu su sake zabarshi a zaben shekarar 2019 me zuwa.

Agege yace, Saraki da mutanenshi sunyi ta addu'ar Allah yasa Buhari ya mutu amma da suka ga basu yi nasara ba shine suka dukufa wajan ganin sun tsigeshi daga mulki, abinda Agege yace shi da abokanshi suka ki amincewa.

Yakara da cewa, muddin suna majalisar to babu wanda ya isa ya tsige Buhari, yanzu sun kori Saraki daga APC saura kuma su tsigeshi daga mukaminshi ya rage, injishi.
Vanguard.

No comments:

Post a Comment