Saturday, 29 September 2018

Zaben fidda gwani: Rivers ta bawa Buhari kuri'u da suka fi na Jigawa

A ranar Juma'a, 28 ga watan Satumba ne jam'iyyar APC ta gudanar da zaben fitar da gwani na takarar kujerar shugabancin kasa a jam'iyyar inda a jihar Rivers aka gudanar da zaben a mazabu 319 kamar sakataren yada labarai na jihar, Mr Chris Finebone ya sanar a Fatakwal


Mr Finebone ya ce ministan sufuri, Chibuike Ameachi yana daga cikin wadanda suka hallarci zaben na fitar da gwani.

A cewar Finebone, mambobin jam'iyyar 388,653 ne a sassa daban-daban da ke jihar suka zabi shugaba Muhammadu Buhari a matsayin dan takarar shugaban kasa da suke so.

"An gudanar da zaben ne ta hanyar amfani da tsarin kato bayan kato kamar yadda kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ta amince da shi.

"Jami'an hukumar zabe mai zaman kanta INEC da ke kananan hukumomi 23 da ke jihar sun hallarci inda ake zabukan.

"Kazalika, jami'an 'yan sanda sun hallarci wuraren da ake gudanar da zabukan domin tabbatar da cewa komi ya tafi lafiya kalau," inji Fishbone.

Mr Ameachi wanda shine jam'in zabe na jihar ya fara ziyarar sakatariyar jam'iyyar kafin ya ziyarci mazubu da ke Fatakwal da kewaye domin ganewa idanunsa yadda abubuwa ke wakana.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment