Friday, 28 September 2018

Zaben Osun: INEC ta bayyana Gboyega Oyetola na APC shi ne zababben gwamna

Hukumar zabe ta Najeriya, NEC ta sanar da cewa Gboyega Oyetola dan takarar gwamna a jam'iyyar APC shi ne ya lashe zaben gwamnan Osun.


Oyetola ya doke Sanata Ademola Adeleke na jam'iyyar PDP da kuri'u 482 bayan da a baya ya sami kuri'u 255,505, inda shi kuma Adeleken ya sami kuri'u 255,023 bayan zabe zagagye na biyu da ya gudana a ranar Alhamis.

Shugaban jam'iyyar PDP a jihar Osun ya yi watsi da sakamakon zaben da hukumar ta INEC ta sanar.

Kola Ologbondinyan, wanda shi ne kakakin jam'iyyar PDP na kasa, ya bayyana cewa kamata yayi a soke zaben gaba dayansa.

Hukumar zaben ta sake gudanar da zaben ne a karo na biyu bayan da ta gano cewa ratar da ke tsakanin jam'iyyar PDP da ta APC (kuri'u 353) ba su kai yawan masu rajista a mazabu bakwan da aka soke zaben ba domin dalilan tashin hankali ko wasu matsalolin na daban.

INEC come fix Thursday 27 September wey dem go do rerun elections for seven polling units inside four local goment for Osogbo, Orolu, Ife South and Ife North local goment.

Saboda haka ne ta tsara yin wannan zaben a ranar Alhamis 27 ga watan Satumba a wadannan mazabun bakwai da ke cikin kananan hukumomi hudu na Osogbo, da Orolu, da Ife South da kuma Ife North.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment