Tuesday, 23 October 2018

2019: APC Ta Samu Biliyan 6.9 Daga Kudin Fom Din Takara

Jam’iyyar da ke mulkin kasar nan  ta APC, ta tara akalla Naira bilyan 6.9 na kudaden sayen fom din takara na masu neman mukaman shugabancin kasa, gwamnoni, da ‘yan majalisun tarayya da na Jihohi.

Jam’iyyar ba ta kai ga shelanta ko nawa ne hakikanin abin da tara tara din ba na fom din takara a jam’iyyar da ta sayar, domin yana wajaba a kanta ne ta bayyana hakan ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa kadai a lokacin da za ta gabatar da bayanan ta na shekara. Sai dai wannan lissafin ya fito ne kawai daga abin da rahoton kwamitin gudanarwar Jam’iyyar ya lissafta. Sannan wannan bai hada da abin da shalkwatar Jam’iyyar ya tara ba na wadanda suka siyi fom din yin takaran majalisun Jihohi 36.

Lissafin ya nu na Jam’iyyar ta APC ta tara Naira bilyan 3.59 ne a wajen wadanda suka siyi fom din yin takaran mukaman gwamna su 160.

Hakanan ‘yan takara 282 da Jam’iyyar ta wanke domin yin takara a kujerun majalisar Dattawa sun siyi Fom na jimillan Naira bilyan 1.95.

Masu neman tsayawa takarar Majalisar wakilai sun siyi Fom din na Naira bilyan 1.39, a sa’ilin da dan takaran neman shugabancin kasar nan kwara daya tilo, Shugaba Buhari ya siyi Fom din a kan Naira milyan 45.

Jam’iyyar ta siyar da Fom dinta na neman tsayawa takarar shugabancin kasar nan ne a kan Naira milyan 45, masu son tsayawa takarar gwamna kuma sun siya a kan Naira milyan 22.5, Naira milyan 7 ne masu son tsayawa takarar majalisar dattijai suka siyi Fom din, sa’ilin da masu son tsayawa takarar majalisar wakilai suka siyi Fom din a kan Naira milyan 3.85.

Jam’iyyar kuma ta bayar da sanarwar yin ragin kashi 50 na kudaden Fom din ga dukkanin mata masu son tsayawa takaran.

Mace guda ce dai ta nemi tsayawa takarar kujerar gwamna, a sa’ilin da mata 21 suka nemi tsayawa takarar majalisun dattijai.

Masu nufin tsayawa takara 160 ne da suka hada da Ministoci biyu suka siyi Fom din don neman tsayawa takarar gwamna a Jam’iyyar, kowanne a kan Naira milyan 22.5, wanda jimlar su ya kai Naira bilyan 3.6.

Jihar Borno ce ta fi kowace Jiha yawan ‘yan takarar na gwamana da ‘yan takara 21, sai Jihar Taraba mai ‘yan takara 12.

Jihar Nasarawa ce ta 3 da yawan ‘yan takara 11, sai Jihohin Gombe, Zamfara, Ebonyi da Imo masu ‘yan takaran na gwamna 9 kowannen su.

Jihar Oyo tana da ‘yan takara 8, Jihar Abiya tana da ‘yan takara 7, sai Jihohin Binuwe, Ogun da Enugu masu ‘yan takaran na gwamna 6 kowaccen su.

Jihohin Yobe, Delta da Kros Riba suna da ‘yan takara 5 ne kowannen su, sai Jihohin Bauci, Sakkwato, Ribas da Akwa Ibom masu ‘yan takara 4 kowannen su, Jihohin Lagos, Katsina da Adamawa suna da ‘yan takara 4 kowannen su.

Jihohin Neja, Jigawa da Kebbi suna da ‘yan takara 2 ne kowannen su, gwamna Solomon Lalong, na Jihar Filato shi kadai ya kasance dan takara a Jam’iyyar a Jihar ta Filato
Leadershiphausa.

No comments:

Post a Comment