Tuesday, 9 October 2018

A karin farko tun bayan da ya fadi zaben fidda gwani, Tambuwal yayi magana akan nasarar Atiku

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal a karin farko tun bayan da ya fadi zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na PDP wanda Atiku ya lashe, ya fito ya taya Atikun murna.


A wasikar da ya aikewa Atikun, Tambuwal ya bayyana cewa, shi da iyalinshi da magoya bayanshi suna taya Atikun murnar lashe zaben da yayi kuma yanda ya lashe zaben ya tabbatar da cewa PDP ta dawo kan kafafunta kuma ta gudanar da sahihin zabe.

Ya tabbatar da cewa, zai bayar da goyon baya ga Atiku dan ganin ya kai ga nasara a zaben 2019.

A wani labarin kuma na gwamna Tambuwal rahotanni sun bayyana cewa ya umarci jami'an 'yansanda na jihar da su kwato motocin wasu kwamishinonin jihar da basu bishi zuwa jam'iyyar PDP ba.


No comments:

Post a Comment