Friday, 12 October 2018

A karin farko Usain Bolt yaci kwallaye 2 a wasa daya

Tsohon turaron dan tseren Duniya, Usain Bolt ya zura kwallaye biyu a karin farko a wasa daya tun bayan da ya koma buga kwallo, Bolt ya saka kwallayen biyunne a wasan da kungiyar da yake tisaye da ita, Central Coast Mariners ta lakadawa Macarthur South West  kwallaye 4-0 a wasan sada zumunta da suka yi.


Tun bayan daina wasannin gudu da yayi, Bolt ya bayyana ra'ayin komawa buga kwallon kafa.

Wannan kungiya ta kasar Australia bata tabbatar dashi a matsayin dan wasanta ba amma dai yana atisaye da itane.

Bayan wasan ya shaidawa manema labarai cewa yaji dadin cin wadannan kwallaye da yayi don dama ya zo nan ne dan ya nunawa Duniya cewa yana kan kara kwazo.

No comments:

Post a Comment