Friday, 26 October 2018

A karo na biyu wata jaridar kasar Ingila tace Buhari ba zai ci zaben 2019 ba, Atiku ne zai yi nasara

Jaridarnan ta kasar Ingila me suna The Economist, a karo na biyu ta sake cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba zai kai labari ba a zaben shekarar 2019 da za'a yi, inda tace abokin hamayyarshi, Atikune zai lashe zaben.


The Economist ta wallafa wannan kintace nata ne da jaridar Thisday ta samu wanda yayi bayani filla-filla akan yanda zaben zai kasance.

A cikin rahoton tace Atiku wanda shine dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP kuma sun fito yanki daya ne da shugaban kasa, Buhari, watau Arewa, akwai yiyuwar zai zo kankankan a yawan kuri'u da Buhari a yankin.

Yayin da a yankin kudu kuma wanda dama can jam'iyyar PDP ce ta fi yin nasara, Atiku zai yi kamfe da rashin aikin yi da talauci da ake fama dashi da kuma matsalar tsaro wajan yin nasara akan Buhari.

Jaridar tace idan aka yi rashin sa'a wannan kintacen nata bai zo daidai ba, watau Buhari ya lashe zabe to PDP ba zata yadda ba zata ce an yi magudi ne.

Ta kuma ce a lokacin zaben za'a samu koma bayar tattalin arziki amma idan Atiku ya lashe zaben, wanda shine ake ganin tsarinshi na gyaran tattalin arziki ya fi kyau, matsalar matsin tattalin arzikin ba zata dade ba zai shawo kanta.


No comments:

Post a Comment