Saturday, 6 October 2018

A karon farko an naɗa mace mukami mafi girma a harkokin banki a Saudiyya

A karon farko a ƙasa mai tsarki an baiwa mace shugabancin wani babban banki dake ƙasar.


Kafafen yaɗa labaran cikin gidan ƙasar ta bayyana cewar bankin Alavval da haɗin gwiwar Saudi English Bank (SBB) sun nata Lubna el- Alyan a matsayin shugaba.

Wannan ne dai karon farko da aka taba baiwa mace mukami mai girma a fannonin bankuna.

Alyan wacce ta ƙware a lamurkan tattalin arziki tana ɗaya daga cikin kwamitin zartarwa na kanfunan Halin da Olayan.

Haka kuma tana ɗaya daga cikin mambobin Kungiyar Kwadagon Saudiyya da kuma Kuma Kungiyar Nazarin Ƙasashen Larabawa.

A shekarun baya ta taɓa zama ɗaya daga cikin majalisar gudanarwa ta bankin Alavval wanda mallakar Saudiyya da Holan ne.

A kwanakin baya ne bankin Alavval da SABB suka rattaba hannu akan tafiyar da aiyuka tare.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment