Saturday, 13 October 2018

Abu 5 game da Peter Obi, wanda Atiku ya zaba yayi masa mataimaki a zaben 2019

Da yammacin ranar Juma'a ne dai muka samu labarin cewa Atiku Abubakar wanda ya lashe zaben fitar da gwani sannan kuma ya samu tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP zabe mai zuwa ya zabi Peter Obi a matsayin mataimakin sa.

Wannan ne ma ya sanya muka nemo maku muhimman abubuwa 5 game da Peter Obi din domin ilmantar da ku game da sanin ko waye shi.
1. Ya taba zama shugaban bankin Fidelity na kasa baki daya yana da kananan shekaru.

2. Ya taba zama shugaban hukumar nan ta hada-hadar kudade ta Nigeria Security and Exchange Commission.

3. Ya yi gwamnan jihar Anambra har sau biyu.

4. Yana shirin yin takarar Sanata ne kafin samun wannan matsayin nashi.

5. Yayi aure a shekarar 1992 kuma yanzu yana da 'ya'ya biyu kacal.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment