Wednesday, 24 October 2018

Abubuwa basu tafiya yanda ya kamata a kasarnan>>Sarkin Musulmi

Sarkin musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar na III yayi tsokaci akan yanda lamura ke gudana a kasarnan inda yace abubuwa basa tafiya yanda ya kamata.


Sarkin ya bayar da misali da fadan Kaduna wanda yayi sanadin salwantar rayuka sama da 50 wanda yace bafa fadan addini bane, saboda ba'a kona coci ko masallaciba, wasu ne marasa aikinyi da suke fama da yunwa suke neman yanda zasu yi da rayuwarsu suka fasa shaguna suna satar abubuwa da kuma kashe wanda basu ji ba basu gani ba.

Sarkin yayi wannan jawabine a Abuja wajan taron da hukumar sasanta tsakani dan ci gaban dimokradiyya ta gudanar, kamar yanda jaridar Punch ta ruwaito.

Ya kara da cewa yanzu da muke tunkarar zabe za"a rika samun irin wannan matsalar saboda wasu 'yan siyasa zasu yi amfani da wannan damar wajan samun nasara ga abokan hamayyarsu.

Sarkin ya bayyana takaici akan yanda babu tsari me kyau akan gudanar da harkar tsaro ta bangaren gwamnatin tarayya sannan kuma su jami'an tsaron babu hadin kai a aikin nasu dan cimma abinda ake so.

No comments:

Post a Comment