Monday, 1 October 2018

Adam A. Zango na murnar zagayowar ranar haihuwarshi: Yace shekarunshi 34: Saidai wani abokin aikinshi yace ya rage 5

A yaune tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango ke murnar zayowar ranar haihuwarshi, ya bayyana cewan yau na cika shekaru 34, ina godiya ga Allah, saidai wani abokin aikinshi yace ba haka bane Adamun ya rage shekaru 5 cikin shekarun nashi.Tauraron me bayar da umarni, Abdulamart mai kwashewa bayan da yaga Adamu yace shekarunshi 34, sai yace, a tara da 5 din da ka cire.

No comments:

Post a Comment