Wednesday, 3 October 2018

Ado Gwanja ya fitar da katin gayyatar aurenshi da ya sha banban da na farko

A makon da ya gabatane muka ga katin gayyatar daurin aure na tauraron mawakin mata kuma jarumin fina-finan Hausa, Ado Isa Gwanja wanda ke dauke da bayanan cewa za'a daura mai aure da sahibarshi, Maiminatu ranar Asabar me zuwa da karfe 11:00, to saidai Adon ya fitar da wani katin da ya sha banban da wanda muka gani.


A katin da ya fitar ta dandalinahi na sada zumunta, Gwanja ya bayyana cewa, ga ainahin katin gayyatar wanda ya bayyana daurin auren nashi ranar Juma'a ne da karfe 4:00PM.

Muna fatan Allah yasa ayi lafiya.

No comments:

Post a Comment