Wednesday, 17 October 2018

A'isha Alhassan ta wa ofishin APC na Taraba tumbur: Ta kwashe duk kayan da ta basu kyauta

Tsohuwar ministar mata, Hajiya A'isha Alhassan ta kwashe duk kayan da ta bayar kyauta ga ofishin jam'iyyar APC na jihar Taraba, abubuwn da ta kwashe sun hada da, darduma, na'urar sanyaya daki, tebura duk ta kwashe kayanta.


Sakataren hulda da jama'a na APC a jihar ta Taraba, Mr Aaron Artimas ya bayyanawa kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN haka a wata hira da suka yi dashi.

Yace abin ya basu mamaki kuma abin kunyane gareta dan kuwa ace minista guda wadda kuma ta ci albarkacin wannan jam'iyya amma ta kaskantar da kanta zuwa irin wannan abu gaskiya be dace ba.

Ya kara da cewa, sun bata damar kwashe kayanta da ta bukaci hakan, kuma ta yiwa ofishin nasu tumbur, dan komai data bayar ta kwashe, su kuma sun tsaya suna kallo cikin mamaki.

Da aka tuntubeta, A'isha tace ita bata sa a kwashe wannan kaya ba amma taji dadin hakan.

Ta kara da cewa, masoyantane suka bukaci kwashe wadannan kaya ita kuma tace musu suje su kwashe, tace, da ace da kashin kanta ta bar jam'iyyar to da babu matsala dan wadannan kaya da ta bayar zata iya bar musu amma kowa ya ga abinda ya faru.

Jam'iyyar APC dai ta hana A'isha Alhassan wadda aka fi sani da Mama taraba tsayawa takarar gwamnan jihar dalilin haka ita kuwa ta fice daga jam'iyyar.

No comments:

Post a Comment