Tuesday, 23 October 2018

A'isha Buhari ta hana shugaban APC shiga fadar shugaban kasa

Uwargidan shugaban kasa A’isha Buhari, ta haramta wa shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole shiga fadar shugaban kasa da ke Abuja.


A’isha Buhari dai ta yi wa Oshiomhole katanga da shiga harabar gidan su na zama da ke cikin fadar ta shugaban kasa, inda ta ce muddin Oshiomhole ya na da bukatar ganawa da Mai gidan ta, to lallai ya ja linzamin dokin sa iyakar ofishin sa ba tare da ya karasa zuwa gidan su ba.

Uwargidan shugaban kasar dai ta fusata da Oshiomhole ne, dangane da yanayin jagorancin da ya ke yi wa jam’iyyar APC, inda a halin yanzu ta na daya daga wasu makusanta Shugaba Buhari da wasu gwamnonin jam’iyyar da ke yunkurin tumbuke shi daga kujerar sa.

A’isha Buhari ta ba jami’an tsaro umarni su yi wa Oshiomole katanga daga shiga harabar gidan su na zama da ke cikin fadar shugaban kasa.
Sarauniya.

No comments:

Post a Comment