Thursday, 4 October 2018

Akwai hannun manya ko dattawan jihar Filato a cikin rikicin jihar>>Buratai

Babban hafsan sojin kasan Nijeriya, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai, ya bayyana cewar akwai hujjoji karfafa dake  tabbatar da Kungiyoyin ta'addanci na kabilu a jihar Filato wanda manyan mutane ko dattawan jihar ke daukar nauyin su. 


Buratai ya baiyana haka ne jiya lokacin da ake bison gawar wasu sojoji guda 3 wadanda aka kashe a rikicin daya barke a ranar 6 ga watan Satumba a karamar hukumar Barkin Ladi. 

Komandan rundunar "Operation Safe Haven", Major-General Augustine Agundu, shi ya wakilci Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai yayin bison Sojojin wanda ya gudana a barikin Rukuba.
Rariya.

No comments:

Post a Comment