Saturday, 20 October 2018

Ali Nuhu ya wa Karkuzu sha tara ta arziki

Tauraron fina-finan Hausa, Ali Nuhu ya tallafawa abokin aikinshi, Karkuzu da kudin haya a yayin da dan wasan fina-finan Hausan ya shiga halin kaka nikayi akan gurin zama.


Marubuciya kuma ma'aikaciyar gidan talabijin na Arewa24, Fauziyya D. Sulaiman ta bayyana yanda abin ya faru kamar haka:

Alhamdullahi, Jarumi Ali Nuhu ya turo da kudi Naira dubu hamsin (50k). A baiwa Baba Karkuzu ya biya kudin hayar gida. Allah ya saka da alkairi. Kafin faruwar wannan lamarin Baba Karkuzu yana zaune ne a gidan abokinsa shekara da shekaru, sai dai bayan mutuwar abokinsa nasa yaransa suka tashe shi, Wanda hakan ya saka shi shiga matsala domin girma ya kama shi. Allah ya saka da alkairi bisa wannan taimakon# Ali Nuhu. Amin.

No comments:

Post a Comment