Tuesday, 2 October 2018

Allahu Akbar: Yadda Marigayi Baba Ari ya karkatar da jirgin sa daga cikin mutane kafin mutuwar sa

Majiyar mu ta sirri a rundunar sojojin saman Najeriya ta labarta mana irin jarumtar da marigayi matukin jirgin nan na rundunar, Baba Ari ya nuna lokacin da jirgin sa yayi tsari da na 'yan uwan sa a garin Abuja cikin satin da ya gabata.


Kamar dai yadda muka samu, majiyar ta mu tace Marigayin ganin cewa jirgin nasa ya kwace kuma babu makawa sai a fado sai yayi anfani da basira irin wadda aka san shi da ita ya karkatar da jirgin daga cikin mutane ya zuwa wurin da ba kowa.

Wannan dai ba karamar dubara bace yayi inda hakan ya sa babu farar hula ko daya da hatsarin ya rutsa da shi sai dai su dake a ciki kawai.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa shugaban kasar Najeriya ma, Muhammadu Buhari yayi jimamin rasuwar sa tare da yin addu'a samun rahama ga mamacin.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment