Wednesday, 3 October 2018

Ambode ya amince da shan kaye a zaben fid da gwani na Lagos

Gwamnan jihar Legas da ke kudancin Najeriya Akinwunmi Ambode ya amince da shan kayen da ya yi a zaben fid da gwani da aka yi na takarar gwamna na jam'iyyar APC.


Kwamitin kula da harkokin zabe da uwar jam'iyyar APC ta tura zuwa Legas domin gudanar da zaben fitar da gwani ne ya sanar da sakamakon zaben da aka yi ranar Talata, inda ya ce Alhaji Babajide Samwo-Olu ne ya lashe zaben.

Shugaban kwamitin Clement Ebiri ya ce Alhaji Samwo-Olu ya lashe zaben da kuri'u 970,851 yayin da gwamna mai ci Akinwunmi Ambode ya samu kuri'u 72,901.

Da farko dai Gwamna Ambode ya yi watsi da sakamakon zaben, amma daga bisani a ranar Laraba bayan wani taron manema labarai, sai ya amince da shan kaye.

A wata sanarwa da aka aike wa manema labarai bayan taron, Mista Ambode ya ce lokaci ya yi da jihar za ta ci gaba da abin da ke gabanta, bayan shafe kwanaki ana kai-komo a harkokin siyasa.

Ya kara da cewa: "Ya kamata mu mayar da hankali wajen yin abin da ya kamata na gaba don ka da mu yi asarar nasarorin da muka cimma cikin shekara uku da rabi da suka gabata.

"Ya ku mutanen Legas, APC babbar jam'iyya ce kuma ya kamata bukatar jiharmu kullum ta kasance kan gaba fiye da duk wani mutum ko kungiya.

"A don haka ne nake yi wa wanda ya lashe zaben nan na fid da gwanin takarar gwamna Mr. Babajide Sanwo-Olu, murna da zuciya daya, kan nasarar da ya samu, ina kuma kira ga jama'ar jihar nan da su mara wa dan takarar gwamna na jam'iyyarmu baya a zaben 2019," a cewar Ambode.

Gwamnan ya kuma sha alwashin yin duk abin da ya dace don tabbatar da mika mulki cikin kwanciyar hankali ga sabon gwamnan da zai lashe zabe a watan Mayun 2019.

"Don haka ina kira ga dukkan mambobin jam'iyyarmu da mu zama tsintsiya madaurinki daya, mu mara wa dan takararmu baya, don mu ciyar da jihar nan tamu gaba.

"Ci gaban Legas shi ne gaba da komai. Abu ne da na dauki shekara uku da rabi ina aiki a kansa, kuma zan ci gaba da ganin an yi nasara kan hakan."Ina kuma so na yi amfani da wannan damar don gode wa jagoranmu na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da shugabancin jam'iyyarmu a matakin jiha da kasa baki daya da dukkan al'ummar Legas."

'Yan takara biyu ne suka fafata a zaben fidda gwanin da suka hada da Akinwunmi Ambode da kuma Jide Sanya-Olu.

An yi ta samun takaddama a zaben
Batun fidda dan takarar gwamnan APC a Legas na daya daga cikin rikicin jam'iyyar da ya yi ta jan hankali, kasancewar alamu da suka nuna uwayen jam'iyyar a jihar ba su goyon bayan Gwamna Ambode.

Gabanin zaben fitar da gwanin, 'yan takarar fid da gwanin na APC a Legas sun yi musayar kalamai masu zafi tare da kuma zargin juna.

A wani taron manema labarai a ranar Lahadi ma Mista Ambode ya zargi Alhaji Babajide Sam-Oulu da cewa mutum ne da aka kama da laifin amfani da kudin jabu a Amurka har aka daure shi, da kuma cewa ya taba samun tabin hankali.

Amma a martaninsa Alhaji Babajide ya kame bakinsa yana cewa shiru ma magana ce, yana mai cewa uwar jam'iyyar APC ce za ta mayar da martani.

Masu lura da al'amura dai sun yi ta hasashen cewa sakamakon zaben fid da gwanin zai yi tasiri sosai ga makomar karfin uban jam'iyyar Bola Ahmed Tunibu idan har wanda yake mara wa baya ya yi nasara ko kuma sakamakon ya rage tasirinsa a siyasar jihar idan har Ambode ya yi nasara.
BBChausa.
No comments:

Post a Comment